ABNA24 : Rahotanni daga Nijeriya ɗin dai sun nuna cewa cikin kwanaki shidan da suka gabata babu wani da ya mutu daga cutar, kamar yadda adadin waɗanda suke kamuwa ɗin ma ya ragu sosai.
A bisa sanarwar da Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriyan NCDC ta fitar ta ce mutane biyar sun mutu a jiya Alhamis lamarin da ya sanya adadin waɗanda suka mutu a Nijeriya sakamakon wannan cutar ya kai mutane 2,036.
Har ila yau hukumar ta ce cikin awanni 24 da suka gabata an samu wasu mutane 97 da suka kamu da cutar wanda hakan ya sanya adadin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar tun bayan bayyanarta suka kai mutane 162,275.
Cikin makon da ya gabata dai adadin waɗanda suke kamuwa da cutar a kowace rana yana yin ƙasa sosai.
A sabuwar ƙididdigar dai jihar Lagos har ila yau ita ce a kan gaba da mutane 50 sai kuma Kaduna da mutane 12 da kuma Abuja da mutane 10.
342/